Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Quattara sun kai hari kan gidan Gbagbo a Ivory Coast


Hayaki ya turnuke a birnin Abidjan, 6 ga watan Aprilu
Hayaki ya turnuke a birnin Abidjan, 6 ga watan Aprilu

Dakarun da ke biyayya ga mutumin da duniya ta ayyana a matsayin shugaban kasar Ivory Coast sun kai hari kan mabuyar karkashin kasar bijirarran shugaban a jiya Laraba

Dakarun da ke biyayya ga mutumin da duniya ta ayyana a matsayin shugaban kasar Ivory Coast sun kai hari kan mabuyar karkashin kasar bijirarran shugaban a jiya Laraba, amma su ka janye daga baya. Dakarun da ke biyayya ga Alassane Ouattara sun kaddamar da hari kan gidan Laurent Gbabgo bayan ya ci gaba da kin amincewa da shan kaye a zabe da kuma mika wuya. To sai dai kuma, sun gamu da turjiya sosai daga dakarun Gbagbo, duk ko da yake akasarin sojojin kasar sun yi saranda. Shaidun gani da ido sun ce sun ji karar wutar bindiga da bama-bamai daga gidan, inda ake kyautata zaton Gbagbo da iyalansa na nan labe cikin dakin karkashin kasa. Fadan ya lafa da yammacin jiya Laraba. Shaidun sun ce mayakan Ouattara sun ja da baya.Wani mukarrabin Mr. Ouattara yace an umurci dakarun sun damke Mr. Gbagbo da ransa. Mai magana da yawun Mr. Gbagbo yace cikin wadanda su ka kai harin har da sojojin Majalisar Dinkin Duniya da kuma tsohuwar uwar gijiyar mulkin mallakar Ivory Coast wato Faransa, zargin da wani jami’in gwamnatin Faransa ya karyata. Ivory Coast ta shiga fama da rikicin siyasa tun daga watan Disamba, bayan da Mr. Gbabgo ya ki amincewa da sakamakon zaben da ya nuna cewa mutanen Ivory Coast sun zabe Mr. Ouattara a matsayin shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG