Wani sojan kasar mai mukamin kanar, Ahmed Mohammed, ya gayawa Sashen harshen Somalia na Muryar Amurka cewa, sun kai somamen ne a wani wuri kusa da garin Masagawa wanda yake kusa da El-Dheer, a yankin da ake kira Galgadudd. Yace an kashe sojan gwamnati daya a matakin.
Mazauna Masagawa sun gayawa Sashen Somaliyacewa, sun ji karar wasu fashe fashe masu karfin gaske, yayinda sojojin gwamnati suke gwabzawa da mayakan sakan na al-Shabab.
An dauki wannan matakin ne a dai dai lokacinda shugabannin gwamnatin kasar da na jihohi suke wani taro a Baidoa, babban birnin lardin yankin Bay,dake kudu maso yammacin kasar, domin su tattauna kan batun tsaro lokacin zaben kasar da aka ayyana cikin watan Agustan bana.