Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Jami'o'in Nijar Na korafi Akan Yajin Aikin Malamansu


Shugaban Nija Mahammou Issoufou
Shugaban Nija Mahammou Issoufou

Yajin aikin na baya bayan nan da malaman jami'o'in Nijar suka fantsama ciki shi ne na biyu cikin wannan watan Satumba

Yajin aikin na yanzu ya faru ne a washegarin taron manema labarai da ministan ilimi mai zurfi Umaru Muhammad ya kira domin sanar da al'ummar kasar cewa gwamnati ta biya mafi yawan albashin malaman da kudaden bincike da malaman ke binta.

Amma kungiyar malaman jami'o'i mallakar gwamnati ta bakin babban sakatarenta Bala Adare ya shaidawa Muryar Amurka cewa labarin ba haka yake ba. Yace gwamnati bata cika alkawarinta ba.

Tuni yajin aikin na mako daya ya fara yin tasiri a harkokin koyaswa a jami'ar Abdulmummuni dake Yamai inda shugabannin kungiyar dalibai suka fara nuna damuwa a kai.

Shebu Sallau sakatare janar na kungiyar dalibai yace yajin aikin yana bata masu lokaci da shafar karatunsu. Yace baicin malamansu su kansu suna cikin matsalar rashin biyansu alawus dinsu da ake basu watanni ukku ukku. Ya kira gwamnati da ta dauki matakan da suka dace a warware matsalar.

Shi ma Samaila Alhassan yace ana kara masu lokacin karatu kafin su kare.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG