Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Coats Yace Bai Kamataba Ya Bayyana Tattaunarsa Da Shugaba Trump Ba


A wani taron manema labarai da aka yi, daraktan hukumar leken asirin Amurka ba ce kala ba akan zarigin cewa shugaba Trump ya tuntube shi akan binciken Rasha.

Jami’in dake kula da ayyukan leken asirin Amurka ya ki yin bayani dangane da rahotannin da kafafen yada labara ke yadawa cewa shugaba Donald Trump ya matsa masa da ya karyata yiwuwar alaka tsakanin jami’an kemfe din Trump da Rasha a fili, a lokacin zaben shugaban kasa a Amurka cikin shekarar 2016.

Daraktan Ma’aikatar tsaron Kasa Dan Coats, ya fadawa Kwamitin ‘yan majalisa cewa, “ganin matsayin da nake akai da kuma irin bayanan da nake ba shugaban kasa, bai dace ba inyi bayani a bayyane akan wannan al’amari, bana jin ya dace in bayyana tattaunawa ta da Shugaban kasa.”

Daga baya Coats ya ce ba ba ya da ja akan ingancin binciken da ake yi akan Rasha ba, ya kara da cewa an abinciken ne don gano bakin zaren,” yadda kasar za ta maida hankali akan wasu batutuwan.

Kwanan nan, kafafen yada labarai suka bada rahoton cewa Trump ya nemi Coats da kuma Daraktan ma’aikatar tsaron kasa Michael Rogers, su karyata zargin da ake na katsalandan Rasha a zaben da ya gabata domin taimakawa Attajirin samun nasarar Shiga White House.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG