Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Ibro Ya Rasu


Rabilu Musa Dan Ibro
Rabilu Musa Dan Ibro

Shahararren dan wasan barkwanci na Hausa, Rabilu Musa wanda aka fi sani da sunan Dan Ibro ya rasu.

Larabannan ne da safe Dan Ibro ya rasu a wani asibiti a Kano, bayan jimawa yana fama da rashin lafiya.

Rahotanni da dumi-duminsu daga Kano na cewa an kai gawar shahararren dan wasan barkwanci na Hausa, Rabilu Musa Danlasan, wanda aka fi sani da sunan Dan Ibro, zuwa gidansa, inda aka yi mishi jana’iza.

Wasu rahotanni sun ce marigayin bai jima da komowa Najeriya daga jinya a wata kasar waje ba.

An sha yayata labarai wadanda ba na gaskiya ba a game da rasuwar Dan Ibro a can baya.

XS
SM
MD
LG