Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar-Bakin-Wake Ya Kai Hari Kan Kwambar NATO A Birnin Kabul


Dan kunar-bakin-waken ya kashe mutane akalla 18, cikinsu har da sojojin NATO su shida, biyar Amurkawa daya kuma dan kasar Canada

Wani dan harin bam na kunar-bakin-wake ya kai farmaki kan wata kwambar motocin NATO talata a birnin Kabul, ya kashe mutane akalla 18, cikinsu har da sojojin NATO su shida wadanda suka hada da Amurkawa biyar da dan Canada daya.

Dan harin bam din ya tayar da bama-baman dake cikin wata motar daukar kaya a kusa da wasu gine-ginen gwamnati a daidai lokacin da jama'a ke kokarin zuwa wuraren ayyukansu da safiya. Tashin bam din ya lalata motoci fiye da 10 na fararen hula da na soja, ciki har da wata bas a babban birnin.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wannan harin.

Jami'an Afghanistan sun ce an kashe fararen hula su 12, wasu akalla 47 suka ji rauni, cikinsu har da mata da yara kanana.

Babban sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO, Anders Fogh Rasmussen, yayi tur da harin na jiya talata, ya kuma ce har yanzu kungiyar tana kan kudurin ci gaba da ayyukanta na kare al'ummar Afghanistan da kara karfin kasar Afghanistan wajen yakar ta'addanci.

Fadar WHite House ta ce babu abinda kungiyar Taliban ta ke haifar ma al'ummar Afghanistan im ban da "kisa da hallaka" kuma har yanzu gwamnatocin Amurka da Afghanistan su na kan bakarsu ta wanzar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar Afghanistan.

Shugaba Hamidu Karzai na Afghanistan shi ma yayi tur da harin, wanda shi ne mafi muni a kan sojojin kasashen waje a Kabul, tun lokacin da aka kashe sojojin Italiya su 6 a watan Satumbar bara.

XS
SM
MD
LG