Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Majalisar Amurka Ya Ziyarci Najeriya Domin Tattara Bayyanai Akan Fataucin Mata


Christopher Smith, Dan Majalisar Amurka
Christopher Smith, Dan Majalisar Amurka

Dan majalisar dokokin Amurka Christopher Smith ya kai ziyara Najeriya domin tattara bayyanai akan fataucin mata da nufin sanin irin taimakon da kasarsa zata bayar domin a shawo kan lamarin.

Dan Majalisa Christopher Smith yayi taron manema labarai a filin da masu zaman durshen neman a kubutar da 'yan matan Chibok da har yanzu 'yan Boko Haram na garkuwa dasu suke.

Su dai masu zanga zangar lumana din suna yi ne domin matsawa gwamnatin kasar ta kara karfi da karfe ta ceto 'yan matan da aka sace. Yayin da yake jawabi Christopher Smith yace ya zo ne domin ya tattara bayyanai da suka shafi fataucin mata a Najeriya da kuma taimako da yakamata a ba kasar wajen ceto 'yan matan Chibok.

Christopher Smith yace ya gana da 'yan majalisun Najeriya da shugabannin kwamitoci da wasu shugabannin addinai yace kuma ya samu bayyanai sosai. Yace to saidai sun lura cewa ta'adanci na karuwa a duk fadin duniya maimakon ragewa duk da kokarin da a keyi a wurin maganceshi.

Christopher yace zai koma Amurka su sake zama a kwamiti su gabatar da rahoto akan ziyararsa. Yace amma fa a tuna alhakin ceto 'yan matan ya rataya ne akan mahukuntan Najeriya.

Nasiru Gambo daya daga cikin masu zanga-zangar a ceto 'yan matan Chibok yace sai fa an canza salo. Yace wannan lamarin zai cigaba da faruwa har sai gwamnati ta daina dora laifi akan wasu ko wani abu an fuskanci anihin ita matsalar da gasken gaske. Shugabannin yanki da na kasa yakamata su ajiye addini da siyasa da kabilanci gefe daya su yadda da matsalar. Matuka ba'a yi haka ba, ba za'a cigaba ba.

Ga rahoton Medina Dauda.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG