Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Takarar Shugaban Kasar Ghana Na APC Ya Kira Shugabar Hukumar Zabe Tayi Murabus


Hotunan wasu 'yan takaran zaben Ghana da za'a yi watan gobe
Hotunan wasu 'yan takaran zaben Ghana da za'a yi watan gobe

A kasar Ghana, dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar “All Peoples Congress” ko kumaA-P-C, Hassan Ayariga, wanda sau biyu ana haramta mishi tsayawa zabe, yayi kira akan shugaban Hukumar Zabe ta kasar, Charlotte Osei, da ta hanzarta sauka daga kan mukamintatun kafin ayi zaben shugaban kasar da ake shirin yi a watan Disambar nan mai zuwa.

Idan kuwa bata sauka ba, Ayariga yace zaben da za’ayi ran 7 ga watan na Disamba, ba zai kasance na adalci ba.

Sai dai kuma kungiyoyin sa-kai da dama na Ghana da kuma jami’an Hukumar Zaben kanta duk sunyi watsi da wannan kiran na Ayariga, inda suka ce shugabar ta jima tana aiwatar da dokokin zaben Ghana ba tareda nuna son kai ba.

A cikin makon nan ne dai Hukumar Zaben ta Ghana ta bayyana sunayen ‘yan takaran jam’iyyun siyasa bakwai da aka yardar wa shiga zaben shugaban kasan mai zuwa – sai dai shi Ayariga baya cikinsu, da yake Hukumar tace bai cika ka’ikdojin tsayawa ba.

Akan haka ne ya shigar da kara kotu inda kotun ta yarda da matsayinsa amma duk da haka, Hukumar zaben ta yanke shawarar hana mishi tsayawa zaben.

XS
SM
MD
LG