Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangantakar Kasar Cuba da Amurka


Wata tawagar wakilan majalisar dokokin Amurka data dawo daga ziyara data kai Cuba, tace shugaban kasar Raul Castro, ya nuna sha'war ci gaba aiki domin inganta dangantakada Amurka, duk da alwashin da shugaban Amurka Donald Trump yayi na canza alkiblar danganataka tsakanin kasashen biyu.

Senata Patrick Leahy, wanda ya juma yana da'awar ganin an inganta danganataka tsakanin Amurka da Cuba, ya gayawa maname labarai jiya Laraba cewa, Castro ya nuna sha'awar ci gaba da aiki kan sauye sauye a kasar ta fuskar kasuwanci.

Senata Leahy ya kara da cewa, shugaba Castro ya baiwa tawagar kofin jawabi da ya gabatar cikin watan jiya a jamhuriyar Dominican, inda a ciki bayyana sha'awar aiki da shugaba Trump.

A shekara ta 2014 tsohon shugaban Amurka Barack Obama da Ra'ul Castro suka fara daukar matakai na sake daowa da dangantaka tsakanin kasashen biyu bayan da AMurka ta tsinka huldar difilopmasiyya da askar a shekara 1961.

Mr. Obama ne shugaban ASmurka na farko a cikin shekaru 88 da zai kai ziyara zuwa Havana cikin watan Maris na bara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG