Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangantakar Rasha Da Kasar Syria


Wani yana nuna adawa da kaiwa Syria yaki
Wani yana nuna adawa da kaiwa Syria yaki

Farfesa Boube Namaiwa na jami’ar Anta Diop Dakar, Sanegal ya bayyana cewa, akwai kwararan dalilai guda biyar da suka sa Rasha taje jan kafa a batun daukar mataki kan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Masana sun bayyana dalilan da yasa Rasha bata goyon bayan kaiwa Syria hari. A cikin hirarsu da Sashen Hausa, Farfesa Boube Namaiwa na jami’ar Anta Diop Dakar, Sanegal ya bayyana cewa, akwai kwararan dalilai guda biyar da suka sa Rasha taje jan kafa a batun daukar mataki kan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Na farko yace, Rasha tana da dadadden tarihin hulda da kasar Rasha tun zamanin tsohon shugaban kasar, mahaifin Bashar, watau Hafiz Al-Assad. Na biyu bisa ga cewar Frofesa Boube Namaiwa, Rasha tana gani kamar akwai munafunci a ciki. Tana ganin kamar ana bada karfi ne kan abinda gwamnatin Syria ke yi ba tare da kula da abinda ‘yan tawayen ke aikatawa ba.

Dalili na uku inji Farfesa Namaiwa shine, Rasha da China suna yunkurowa, suna so su taka rawa can dabam ba irin wadda kasashen turai suke takawa ba. Watau sun zama kamar kishiya ne da Amurka. Saboda haka duk abinda Amurka zata yi zasu ce ba daidai bane.

Na hudu kuma shine, suna shakkun abinda zai biyo bayan kaiwa Syria hari, sabili da sun ga an yi a Iraq, an yi a Libya, an yi a Afghanistan, an yi a Masar, amma duk ba a sami zaman lafiya ba a kasashen. Kuma dukansu kasashe ne wadanda da suke karkashin taron Soviet. Suna gani kamar kasashen dake cikin wannan kungiyar ne a da, ake bi ana yiwa wannan alhali kuwa akwai wadansu kasashen da ba a kulawa da abinda suke yi, suna da sarauta da ba irinta damokaradiya ba amma ba a taba su.

Dalili na karshe da yake yiwa yasa Rasha bata goyon bayan kaiwa Syria hari bisa ga cewar Frofesa shine, suna gani kamar ana kare Isra’ila ne kuma ana neman a raunana kasashen Labarawa ne domin Isra’ila ta bunkasa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00
Shiga Kai Tsaye
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG