Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok Ta Kubuta Daga Hannun Boko Haram


BOKO HARAM: Bikin murnar sako wasu 'yan matan Chibok
BOKO HARAM: Bikin murnar sako wasu 'yan matan Chibok

Rahotanni na cewa ‘daya daga cikin ‘dalibai ‘yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace shekaru biyu da suka gabata ta kubuta.

Mai magana da yauwan shugaban Mohammadu Buhari, Femi Adesina, bai bayar da wani cikakken bayani ba, amma ya ce Sojojin Najeriya ne suka samo yarinyar kuma suka ‘dauketa zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Kubutar ‘dalibar dai yazo ne makonni biyu bayan da kungiyar Boko Haram ta yi wa gwamnatin Najeriya musayar ‘yan mata 82 ita kuma ta saki fursuna. Cikin ‘yan kwanaki masu zuwa ake kyautata tsammanin ‘yan matan zasu sake haduwa da iyayensu.

Kungiyar Boko Haram ta sace ‘dalibai ‘yan mata 276 a makarantar sakandare ta Chibok, a shekarar 2014, wanda ya tayar da hankulan Miliyoyin mutane a fadin Duniya.

An saki ‘yan mata 21 a watan Oktoba, yayin da wasunsu da dama suka kubuta ‘daya bayan ‘daya.

Amma dai har yanzu ‘yan mata sama da 100 suna hannun Boko haram.

Kungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane a shekaru 8 da ta kwashe tana tayar da hankali a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG