Accessibility links

Yayin da rikicin kasar Syria ke kokarin shiga shekaru biyar da farawa, kasar Amurka ta ce lokaci ya yi da za a nemi mafita kan rikicin kasar.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce lokaci ya yi da za a samu matsaya guda da shugaban Syria Bashar al- Assad kan yadda za a shawo kan rikicin kasar da ya lakume rayuka da dama.

Kalaman na Kerry na zuwa ne yayin da rikicin kasar ke shirin shiga shekara ta biyar da farawa lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane ya kuma janyo ficewar sama da mutane miliyan daya daga muhallansu.

Da yawa suna zargin cewa kungiyar ISIS ta samo asali ne sanadiyar yakin Syria wanda mayakan sa kai suka yi amfani da damar yakin kasar su ka dauki makamai.

A shekarar da ta gabata yarjejeniyar kawo karshen rikicin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka su ka yi kokarin cimma ya samu cikas bayan da aka kasa samun matsaya.

A baya an zargi dakarun gwamanti da yin amfani da makamai masu guba wajen kai hare-hare akan ‘yan tawaye da ke son Assad ya sauka daga kan mukaminsa.

XS
SM
MD
LG