Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Rasha da Ukraine Su Yi Aiki Tare Domin Rage Zaman Dar-dar - Kerry


John Kerry , Sakataren Harkokin Wajen Amurka
John Kerry , Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya gayawa taron ministocin harkokin waje na kasashen dake turai, cewa tilas ne Rasha da Ukraine dukkansu biyu suyi aiki domin sassauta zaman dardar kuma su sake farfado da yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine.

Jiya Alhamis ne Mr. Kerry yayi magana a taron shekara shekara na ministocin harkokin waje na kasashen da suke majalisar tsaro ta turai ko NATO. Taron na kwanaki biyu ana yinsa ne a birnin Belgrade na kasar Serbia.

Ranar Laraba Kerry ya ziyarci Kosovo d a Serbia, inda ya gana da manyan jami'an gwamnatin kasashen.

Yanzu kuma nan ba da jumawa ba, mata anan Amurka zasu sami sukunin gudanar da dukkan ayyukan da ada maza kadai ne suke yi a fagen yaki.

Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter ne ya bada sanarwar haka jiya a Alhamis a helkwatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon.

Mata sun juma suna kutsawa tun a wajajen 1970, lokacinda a karon farko aka basu damar shiga makarantun horasda sojoji da kuma shiga aikin soja. A yanzu dai babu sashen da babu mata a rundunar mayakan Amurka illa shiga fagen daga.

Sakataren yace babu yadda za'a yi a wannan karni ace rundunonin mayakan Amurka zasu iya kauda fuska kan rabin al'uma kuma tayi fatar samun ci gaban ayyukanta.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG