Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Zai Tsame Hannunsa Daga Harkokin Kamfanoninsa


Daya daga cikin gine ginen da Donald Trump ya mallaka.
Daya daga cikin gine ginen da Donald Trump ya mallaka.

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya fada a yau Laraba cewa zai tsame kansa daga harkokin kasuwancin Kamfanoninsa baki daya, domin ya maida hankali kan aikin shugabancin kasa ba tare da matsala ba.

Lamarin da ya zama muhimmiyar magana tun bayan zaben sa, shiga harkokin kamfaninsa da kuma gidajen da ya mallaka a kasashen waje da kuma cikin Amurka. Trump ya rubuta a twitter cewa zai kira taron manema labarai a ranar 15 ga watan December, domin tattauna yadda zai aiwatar da hakan.

Haka nan kuma a yau larabar ne aka ayyana Shugaban Kamfanin Goldman Sachs Steven Mnuchin a matsayin Sakataren Baitil Malin Amurka, sannan Hamshakin Attajiri Wilbur Ross ya ce shi aka zaba ya zama Jagoran Bangaren Kasuwanci.

Trump yana ta aiki tukuru domin cike gurabe a Gwamnatinsa, tun bayan zaben da akayi a ranar 8 ga watan Nuwamba. Daya daga cikin manyan mukaman da ba a cike gurbinsu ba shine Sakataren Harkokin waje, wadanda ake sa ran za a baiwa wannan mukami sun hada da tsohon gwamnan Jihar Massachusetts Mitt Romney, Tsohon Magajin garin New York Rudy Giuliani, da kuma Sanata daga Jihar Tenessee Bob Corker da kuma tsohon Shugaban hukumar leken asirin tsaron kasa, David Petraus.

Romney ya kasance daya daga cikin masu kakkausar suka ga Trump, amma ya yabi Trump bayan sun zauna zaman cin abincin dare a jiya Talata, Inda ya kira tattaunawarsu “ Mai Bude ido da kuma ban mamaki da kuma fahimtar juna.

XS
SM
MD
LG