Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Na Fuskantar Barazanar Mutuwa Sakamakon Yunwa a Habasha Da Somalia


Hukumomin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) sun bukaci kungiyoyin taimako na kasa da kasa, dasu taimaka da kudi domin gudanar da ayyukan ceton rayukan jama’a a sassan da matsalar fari ta rutsa dasu a kasashen Habasha da Somalia, inda yanzu haka dubban mutane ke fuskantar barazanar mutuwa sakamakon yunwa.

Yau shekaru 5 bayan da mummunan karancin abinci na shekarar 2011, ya yi dalilin mutuwar mutane sama da dubu 260 a kasar ta Somalia. Kuma yanzu haka fari ya kara kunno kai a kasar.

Inda wannan lamari yafi Kamari shine yankin Arewacin Puntland da kuma Somaliland, inda yanzu haka rahotanni ke bayyana cewa an samu mace-mace wanda keda nasaba da ciwon da wannan yunwar da kuma wasu ciwarwata masu nasaba da ita ke haifarwa.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD Leo Bobbs, ya ce ko a ranar lahadi data gabata mun samu labarin mutuwar mutane 38 sakamakon wannan matsalar ta yunwa kuma lamarin ya faru ne a yankin Bakool dake kudu maso tsakiyar kasar ta Somalia.

Yace rashin magani da rashin wadataccen abinci da kuma cutar kwalara, musammam ga yara dake wannan yanki na iya karuwa ba tare da samun wani taimakon azo a gani ba.

Yanzu dai kusan rabin ‘yan kasare Somalia na cikin hadari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG