Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubun Dubatan Jama'a Suka Hallara a Birnin Nairobi Domin Ganin Paparoma Francis


Paparoma Francis yana jawabi a Jami'ar Nairobi
Paparoma Francis yana jawabi a Jami'ar Nairobi

Dubun dubatan jama'a ne suka hallara a birnin Nairobi domin addu'a ta musamman da Papa Roma Francis, shugaban darikar Katholika na farko da ya kai ziyara kasar Kenya tun shekarar 1995.

Papa Roma ya je harabar taron a Jami'ar Nairobi cikin motarsa da ake kira da turanci Popemobile ya ratsa da ta cikin gungun bil"adama da suka hallara sa'o'i domin su ganshi.

"Ina kira ta musamman ga matasan kasan nan. Ku lura da muhimmancin al'adun Afirka, da hikima da basira dake tattare da maganar Allah, da kuma kuzari da kyakkyawar tunanin matasa tayi muku jagora wajen aikin gina kasa da al'uma mai aiki d a adalci, dake mutunta ko wane Bil'Adama" inji Papa Roman.

Tunda farko Papa Roman yayi magana ga shugabannin taron musulmi da kirista, inda yace musu tilas ne su rika tuntubar juna kuma su kare matasa daga zama tsagera da tada tarzoma da sunan addini. Da yake magana a ofishin jakadancin Fadar Papa Roma dake birnin Nairobi, yace tuntubar juna tsakanin shugabannin da mabiya addinan biyu, yana da "muhimmanci," ba abu ne na zabi ko shakatawa ba.

Baya ga kokarinsa na kauda gibi tsakanin musulmi da kirista yayin wannan ziyara da yake yi a Afirka, Papa Roma Francis yana kuma magana kan kalubale da duniya take fuskanta daga sakewar yanayi.

Jiya Alhamis Papa Roma yayi kira da a dauki mataki cikin gaggawa domin taka birki ga canjin yanayi, lokacinda ya kai ziyara a ga wata cibiyar aikin kula da muhalli da Majalisar Dinkin Duniya take gudanarwa a birnin Nairobi.

XS
SM
MD
LG