Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Wanda Ba Shi Da Takardar Zama Amurka Za'a Tsare Shi - Jami'in Kwastam


Ginin majalisar dokokin Amurka
Ginin majalisar dokokin Amurka

'Yan majalisar dokokin Amurka sun bayyana cewa wani jami’in shige da fice ya shaida musu cewa duk wani bakon hauren da ba shi da takardar iznin zaman kasa “ya kwana da sanin” za’a tsare shi kuma a mayar da shi kasarsa."

Mukaddashin Darektan hukumar shige da fice da kwastam, Thomas Homan shine ya fada wa ‘yan majilisar wakilai na jamiyyar Democrat su 10 hakan a lokacin da ya gana da su jiya Alhamis a majalisar dokokin kasar.

Sai dai bayan kammala wannan ganawar, dan majilisar wakilai na jamiyyar Democrat daga jihar Texas Joaquin Castro, ya ce burin gwamnatin Trump shine kame bakin haure bakin gwargwadon hali.

Castro ya ce wadanda kawai z asu tsira daga wanna tasku sune yaran da suka shigo Amurka suna kanana kuma yau sun girma kana suna da kariya ta musammam daga wani shirin da tsohon shugaba Barrack Obama ya kirkiro.

A farkon makon da shugaba Donald Trump dai ya hau kan karagar mulki ya ba da umurni na musammam da ya baiwa hukumar shige da fice ikon aiwatar da umurnin.

A halin da ake ciki kuma, daruruwan masu zanga zanga ne suka yi maci cikin dan karen sanyi jiya Alhamis a nan Washington DC, macin da aka kira “ranar da babu baki a Amurka” hadakar da take da goyon baya a duk fadin kasa, har ma wasu masana’antu da ‘yan kasuwa suka rufe kantunansu, domin nuna goyon baya ga bakin.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG