Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniya Ta Yi Tir Da Hare-haren Da Aka Kai Lebanon


Hare-haren da aka kai harabobin masallatai a Lebanon
Hare-haren da aka kai harabobin masallatai a Lebanon

Hukumomin Duniya na cigaba da yin Allah wadai da munanan hare-haren da aka kai Lebanon.

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da tagwayen bama-baman da aka tayar cikin motoci a kasar Labanon jiya Jumma’a, da su ka yi sanadin mutuwar akalla mutane 42 tare da raunata wasu 50.

Kwamitin Sulhun mai mambobi 15 ya yi kira dukkannin ‘yan Labanon da su kare hadin kan kasar a daidai lokacin da wasu ke kokarin illanta kwanciyar hankalin Labanon.

Haka zalika, Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya shawarci ‘yan kasar ta Labanon da su kai zuciya nesa, su cigaba da hadin kai don su karfafa madafun ikon kasarsu,” musamman ma jami’an tsaron Labanon.

Harin na jiya Jumma’a ya auku ne a birnin Tripoli (ko Tarabulus) na arewacin kasar.

Daya daga cikin bama baman ya tarwatse ne a wajen masallacin Taqwa a daidai lokacin da ake gab da kammala sallar Jumma’a. A wannan masallacin ne Sheikh Salem Rafei, na mas’habin Salafiyya mai adawa da mayakan Hezbollah na mas’habin Shi’a da ke Labanon, yakan yi salla. Ba a tabbatar ko ya na cikin masallacin a lokacin ba.

Bam na biyu kuma ya tashi ne bayan kimanin mintuna biyar a wajen masallacin Al Salam da ke Gundumar Al Minna na Tarabulus.

Nan take dai babu wanda ya dai alhakin kai harin. Kungiyar mayakan Hezbollah ta ‘yan Shi’a ta yi Allah wadai da harin, da cewa da alamar wani yinkuri ne na ingiza karin fadan bangarori a Labanon.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG