Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola Ta Kama Wani Dan Jahar Texas A Nan Amurka


darektan babban asibitin Texas
darektan babban asibitin Texas

Wannan ne karon farkon da cutar ta kama wani a cikin kasar Amurka

Hukumomin jahar Texas a kudancin Amurka sun ce wani ma'aikacin kula da lafiya da yayi jinyar mai cutar Ebolar nan dan kasar Laberiya da ya mutu a makon jiya, shi ma ya kamu da kwayar cutar wanda shi ne karon farkon da wani ya yada cutar a cikin kasar Amurka.

Ma'aikatar lafiyar jahar ce ta gabatar da sanarwa a yau Lahadi cewa ranar Jumma'a da daddare ma'aikacin ya ce ya na jin dan zazzabi, wato 'yar masassara kafin gwajin farkon da ya tabbatar da cutar a jikin shi. Amma hukumar yaki da cututtuka da rigakafi ta Amurka CDC a takaice, za ta gudanar da wani gwajin domin ta kara tabbatarwa cutar ce.

Ma'aikacin kula da lafiyar yana cikin ma'aikatan babban asibitin Texas da yayi gwajin da ya tabbatar da cutar Ebola a Amurka a jikin Thomas Duncan wanda ya mutu a makon jiya.

Har wa yau game dai da Ebolar da ta kashe Duncan, yanzu haka jami'an kula da lafiya na ta kokarin ganowa da kuma kula da duk wadanda watakila abun ya shafa bayan da ma'aikacin ya fara gwada alamun kamuwa da cutar.

Tun ba yau ba dai hukumomin kula da lafiya na Amurka ke ta shaidawa Amukawa cewa tsarin kiwon lafiyar kasar ya san yadda zai shawo kan bazuwar kwayar cutar ta Ebola wadda ta halaka dubban mutane a yankin Yammacin Afirka.

Wannan sabon kamuwa da cutar ta Ebola ya bayyana ne a daidai lokacin da filayen jiragen saman Amurka da dama su ka fara zafafa gwajin fasinjoji masu zuwa daga Laberiya da Saliyo da kuma Guinea.

Mahaifiyar Thomas Eric Duncan, dan kasar Laberiya da ya mutu da cutar Ebola a Dallas, a nan ta na tare da Jesse Jackson da wani dan ta
Mahaifiyar Thomas Eric Duncan, dan kasar Laberiya da ya mutu da cutar Ebola a Dallas, a nan ta na tare da Jesse Jackson da wani dan ta

XS
SM
MD
LG