Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

El-Sisi Ya Lashe Zabe


Tsohon hafsin hafsoshin sojin Masar Abdel Fattah el-Sisi ya samu gagarumar nasara a zaben shugaban kasa inda ya kayar da abokin hamayyarshi Hamdeen Sabahi.

Rahotannin farko daga zaben da aka share kwanaki uku ana jefawa, kuma aka kammala jiya Laraba, sun baiwa Sissi sama da kaso 93 cikin 100 na kuri’un da aka jefa. Sabahi wanda ya samu kaso 3 kacal, ya mike kai bori ya hau, yana mai cewa “yayi na’am da abunda jama’ar kasar suke so”.

Sisi dama yana da tabbacin zai lashe zaben tun kafin ranar zabe, kuma ya samu nasarar kiran jama’a su fito su jefa kuri’a, wadanda kiyasinsu ya kai yawan da za’a iya cewa shine yaci zabe, domin ya gyara tattalin arzikin kasar, da kuma kawo karshen rigingimun siyasar Masar.

Jami’ai sunce kaso 46 cikin dari na mutane miliyan 54 wadanda zasu iya jefa kuri’a, sune suka shiga rumfunan zabe, kuma haka ya gaza kaiwa kaso 52 cikin 100 na jama’ar da suka jefa zaben 2012 a lokacin da aka zabi Mohamed Morsi.

Jami’an Tarayyar Turai sunce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, amma akwai ‘yan matsaloli kamar yakin neman zabe a kusa da rumfunan da ake jefa kuri’a.
XS
SM
MD
LG