Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Emmanuel Macron Ya Lashe Zaben Kasar Faransa Da Kashi 65


Emmanuel Macron
Emmanuel Macron

Ya tabbatar cewa kasar Faransa zata ci gaba da kasancewa cikin tarayyar Turai

Emmanuel Macron, ya lashe zaben kasar Faransa da aka gudanar da sagaye na biyu yau, ya doke abokiyar karawarsa Marine Le Pen.

Alkaluman sun nuna cewar Emmanuel Macron, ya samu kashi sittin da biyar (65) inda ita marine Le Pen, ta samu kashi talatin da hudu da digo biyar (34.5) a cikin dari.

Zaben na yau ya kasance zaben da yafi kusan kowane zaben tasiri a tarihin kasar Faransa’

Jim kadan bayan da aka bayyana sakamakon zaben Marine Le Pen, ta shedawa magoya bayanta a wani gidan cin abinci cewa tuni ta kira Emmanuel Macron, domin taya shi murnar lashe zaben da yayi.

Wannan gaggarumin nasarar da Macron ya samu ba zai rasa nasaba da kalaman Marine Le Pen, na neman kasar ta fice daga tarayyar Turai ba da kuma hana Musulmi shiga kasar ta Faransa ba wanda ya ja hankalin duniya ga zaben na kasar Faransa.

Zaben ya kasance zakarar gwajin dafi kuma wani sabon babi a Faransan wannan zamani kuma zai shiga tarihi cewa ;yan Faransa sun zabi canji amma ba juyin juya hali ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG