Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fara Ministan Birtaniya Ya Gargadi Kungiyar Tarayyar Turai


Hoton Fara ministan Ingila David Cameroon, ranar Litinin a wani taron manema labarai a fadar shugaban kasar Ingila.
Hoton Fara ministan Ingila David Cameroon, ranar Litinin a wani taron manema labarai a fadar shugaban kasar Ingila.

Fara Ministan Birtaniya David Cameron, yayi gargadin cewa Birtaniya na iya tsokano jefa nahiyar Turai a cikin yaki muddin ta cimma matsaya akan ta bar kungiyar tarayyar Turai a zaben raba gardama da ake shirin yi awani lokaci nan gaba a cikin wannan shekarar.

Cameron dai yayi wannan Maganar ce yau Littini.

Cameron ya fada yau littini a cikin jawabinsa da yayi akan harkokin tsaron kasa, yayin da ake yekuwar cewa kasar zata jefa kuria a ranar 23 ga wata yuni cewa ko kasar ta Birtaniya zata ci gaba kasancewa cikin kungiyar tarayyar turai mai mambobi 28 ko kuma a’a.

Fara ministan ya jefa tambayoyi game da wannan al'amarin, inda yake cewa “Shin muna da tabbacin cewa zamu ci gaba da samun zaman lafiya a nahiyar mu, anya wannan kalubale abin da zamu iya dauka ne? Sai dai yace ba zai yi saurin yanke hukunci ba akan wannan al’amari.

Kawunan mutanen kasar ta Britaniya sun rabu matuka akan ko kasar tasu ta ci gaba da zama cikin Kungiyar ta tarayyar Turai ko kuma ta fice, kuma daukar ra’yoyi har sau 6 da wasu cibiyoyin bincike suka gudanar kan batun, yana nuna cewa kusan masu son zama cikin kungiyar yawansu daidai yake da masu son a fice.

XS
SM
MD
LG