Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Kara Cafke Karin Wasu 'Yan Ta'ada


Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande

'Yansanda a Faransa sun kara cafke wasu mata da mijinta dangane da mota shake da bam da aka ajiye kusa da wani katafaren mijami'ar Notre Dame dake birnin Paris Lahadin da ta gabata.

'Yandan Faransa sun sake cafke wasu mutane biyu ranar Talata wadanda da aka sani suna da alaka da kungiyoyin dake da tsatsauran ra'ayin addinin Islama.

Motar da suka ajiye kusa da mijami'ar Notre Dame shake da bamabamai bata da lamba lamarin da ya sa ma'aikacin wata mashaya ya tseguntawa 'yansanda. Shi dai wannan ma'aikacin ya lura cewa akwai tukunyar daukan gas da ake girki da ita wurin da ake zamaa bayan motar.

'Yansanda sun kama sun kuma tsare mai motar wanda shi ma nahukunta sun sanshi da tsatsauran ra'ayin addini kuma yana da alaka da 'yan ta'ada. Har yanzu 'yansanda suna neman diyar mutumin saboda ta amsa tambayoyi.

XS
SM
MD
LG