Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransawa Sun Kawar Da Nicolas Sarkozy Daga Kan Mulki


Sabon shugaban Faransa, Francois Hollande
Sabon shugaban Faransa, Francois Hollande

Francois Hollande zai zamo dan jam'iyyar gurguzu na farko da zai haye kan kujerar shugaban kasar Faransa a cikin shekaru kusan 20

Faransa zata yi sabon shugaba a bayan da dan takarar hamayya na jam’iyyar gurguzu Francois Hollande, ya doke shugaba Nicolas Sarkozy na jam’iyyar ‘yan mazan jiya a zaben shugaban kasa da aka yi.

A bayan da aka kidaya kusan dukkan kuri’un da aka kada a zaben fitar da gwanin na jiya lahadi, Mr. Hollande ya lashe kashi 52 cikin 100, yayin da Mr. Sarkozy yake da kashi 48 cikin 100.

Dubban magoya bayan Hollande sun yi gangami su na jinjina masa a shahararren dandalin nan na tsakiyar birnin Paris da ake kira Bastille a takaice. Mr. Hollande, wanda ke adawa da wasu matakan tsuke bakin aljihun da aka dauka a Faransa, ya fadawa jama’ar da ta taru cewa ba wai su mutane ne dake neman canji kawai ba. Ya bayyana su a zaman wani gangamin juyin juya hali dake yaduwa a fadin nahiyar Turai.

Da alamun masu jefa kuri’a na Faransa sun fusata da mummunan rashin aikin yi, kuma irin salon siyasar ‘yan mazan jiya ta Sarkozy yanzu ba ta burge su. Shugaban mai barin gado yace ya dauki alhakin wannan kaye da ya sha.

Mr. Hollande zai zamo shugaban Faransa na farko mai ra’ayin gurguzu a cikin shekaru kusan 20.

Fadar White House ta ce shugaba Barack Obama na Amurka ya buga waya yana taya Mr. Hollande murnar samun nasara, ya kuma gayyace shi da ya ziyarci fadar White House kafin yazo Amurka domin taron kolin manyan kasashe masu arzikin masana’antu da na NATO da za a yi cikin wannan watan.

XS
SM
MD
LG