Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farfado Da Fannin Ilimi A Jihar Adamawa


Bukin Ranar Malamai Ta Duniya A Dakin Taron Kungiyar Malamai Dake Jihar Adamawa
Bukin Ranar Malamai Ta Duniya A Dakin Taron Kungiyar Malamai Dake Jihar Adamawa

Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da kafa dokar ta baci kan fannin ilimi saboda koma bayan da harkar ilimi ke fama da ita, idan aka kwatanta da sauran jihohin Najeriyar.

Kwamishinan ilimi ta jihar Farfesa Kaletapwa George Farauta, itace ta sanar da haka a sakon da gwamnati ta aika taron bukin na ranar malamai da cibiyar kula da ilimi, kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya na wannan shekara a Yola fadar jihar.

Sai dai da take bayyana matsayinta game da gudanar da harkar ilimi, kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Adamawa ta koka da karyewar martaba da kimar da ‘ya ‘yan kungiyar ke da ita a idon gwamnati da jama’ar da ta ke yi wa hidima.

Wadannan sune kalaman shugaban kungiyar kwamrad Rodney Nathan, a bukin ranar da MDD ta kebe tun watan oktoba na alib dubu da casa’in da hudu na wannan shekara mai taken daukaka matsayi da martabar malamai da aka yi a dakin taron kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Yola.

Wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu, ya yi nazarin taken bukin na bana da irin halin da malaman jiha da ke bin gwamnati bashin albashin wata biyar da kuma wasu hakkokinsu tare da la’akari da kima da martabarsu a idon jama’a.

Daga cikin bakin da Sanusi Adamu, ya yi hira da su ciki harda wakilin gwamna Umaru Jibirilla Bindow a taron, shugaban ma’aikatan ofishin gwamna Alh. Abdulrahaman Abba Jimeta, da kuma shugabar makarantar firamaren Luggere Malama A’ishatu Baba Diya, tace rashin daukaka da martaba malamai shine sanadiyar faduwar matsayin ilimi a jihar.

Saurari cikakken rahotan Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

XS
SM
MD
LG