Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farfadowa da Sana'ar Saka a Garin Agayawa Kashi na Karshe


Kayan da aka saka a Agayawa.
Kayan da aka saka a Agayawa.

Malam Abubakar Muhammad daraktan hukumar samar da aiki ko NDE a takaice ya cigaba da bayyana dalilan da suka farfado da sana'ar saka a garin Agayawa.

A cikin sana'a kowace iri ce idan matashi ya koyeta ya kuma riketa to zata rikeshi. Wannan na nufin nan take an fitar dashi daga zaman kashe wando. An fitar dashi daga hannun wani mai mugun nufi da ka iya zuwa yayi anfani dashi.

Yawancin matasan da basu da aikin yi ana sasu kan hanyar da bata dace ba. Irinsu ne ake sawa su yi kashe-kashe da kone-kone da tayar da hargitsi. Duk su ne ake sawa suna abubuwa na abun assha.

Abun da hukumar NDE ke nufi shi ne matasan Agayawa dake cikin karamar hukumar Ingawa da makwaftansu zasu koyi sana'ar domin su samu abun dogaro. Da sana'ar zasu iya farfado da tattalin arzikinsu, su rike mutuncinsu da zaman lafiyan jama'a da ma kasar gaba daya.

Babbar manufar NDE ita ce ta samar ma matasa aikin yi domin su kare rayuwarsu da martabarsu da mutuncinsu da kuma kare zaman lafiya. Matasan Najeriya suna da ilimi da kwazo da hazaka da neman cigaba. Amma idan abubuwa suka rincabe ya zama basu samu abun yi ba to ko za'a fuskanci rashin zaman lafiya.

Biyo bayan da hukumar ta gano sana'ar saka a Agayawa dake son bacewa ta tutubi jihohi daban daban su duba idan akwai wata sana'a data kusan bacewa a jiharsu su shaidawa hukumar NDE. Duk sana'o'in dake neman durkushewa ko bacewa hukumar zata yi kokarin farfado dasu. Koina a Najeriya ashirye suke su kawarda matasa daga zaman banza. Suna son su mayar dasu masu neman na kansu ba sai sun dogara ga kowa ba.

Kawo yanzu kusan jihohi goma sha uku suka tabbatar suna da sana'o'i da suke kokarin bacewa. Hukmar zata farfado dasu kodayake bata da kudin da zata farfado dasu gaba daya.

Ga cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:49 0:00

XS
SM
MD
LG