Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fargabar Ambaliya A Jihohin Sokoto Da Kebbi


Wasu daga cikin gonnakin da ambaliyar ruwa ta mamaye a watan Satumban bara, wacce kuma ta tada mutane milyan 2 daga gidajensu.
Wasu daga cikin gonnakin da ambaliyar ruwa ta mamaye a watan Satumban bara, wacce kuma ta tada mutane milyan 2 daga gidajensu.

Al’ummar jihohin Sokoto da kebbi sunce hankalinsu yana tashe saboda fargabar ambaliya a bana.

Tuna irin masifar da suka shiga a bara a sanadin ambaliyar ruwa, yasa hankalin mutane da daman a jihohin Sokoto da kebbi yake a tashe saboda tsoron abinda zai faru a bana. Wannan fargabar ta biyo bayan hasashen da aka yi na cewa mai yiyuwa ne a sami ruwan sama a wannan shekara fiyeda da na bara. A shekarar da ta gabata dimbin mutane sun rasa muhallansu da gonnaki a sanadin faccewar madatsar ruwa ta Goronyo wacce itace madatsa ta biyu a girma a duk fadin Afrika, Wakilin Muryar Amurka a Sokoto, Murtala Faruk Sanyinna ya zanta da wasu mazuna karamar hukumar Goronyo da suka ce suna cikin damuwa ganin har yanzu ba’a warware matsalolin da suka janyo ambaliyar bara ba. Ga rahoton:

Fargabar Ambaliya A Jihohin Sokoto Da Kebbi

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG