Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA: Platini ba zai tsaya takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta FIFA


Michael Paltini, shugaban hukumar kwallon kafa ta tarayyar turai
Michael Paltini, shugaban hukumar kwallon kafa ta tarayyar turai

Biyo bayan binciken da a ke yi masa Platinin yace ba zai iya tsayawa takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya ba wato FIFA

Michel Platinin, mutumin da ake mai kallon zai gaji shugaban hukumar kwallon kafar duniya, FIFA a da, wato ya bayyana cewa ba zai yi yunkurin tsayawa takara a zaben shugabancin hukumar da za a yi ranar 26 ga watan Fabrairu ba.

Platinin wanda aka dakatar a matsayin shugaban hukumar kwallon kafar nahiyar turai, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Associate Press da kuma jaridar L’ Equipe cewa, koda ya yi nasarar sauya matsayar haramta mai shiga sha’anin kwallon kafa na tsawon shekaru takwas da aka yi, ba shi da isasshen lokacin da zai yi kyakyawan yakin neman shugabancin hukumar ta FIFA.

A cewarsa babu lokacin, sannan babu tsare-tsare da za su bashi damar tsayawa takara daidai da sauran abokanansa da ke neman mukamin.

Burin shugabantar hukumar ta FIFA, ya gushe ga Platini, bayan da aka fara tuhumarsu da zargin karkata akalar wasu kudade da yawansu ya kai dala miliyan biyu, kudaden da aka ce Blatter ya bashi a shekarar 2011.

XS
SM
MD
LG