Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye da mutane dari takwas ne ambaliyan ruwa ya halaka a Pakistan


Hukumomin Pakistan sun ce yawan mutane da suka halaka sakamakon ambaliyar da ruwan sama kamar dab akin kwariya ya janyo yah aura dari takwas.

Jami’an Pakistan sun ce adadin mutane da suka halaka zuwa Asabar, sakamakon ambaliyar da ruwan sama kamar da bakin kwariya ya haddasa, ya ninka, yanzu ya haura dari takwas,yayin da masu aikin ceto suke kokarin kai wa ga dubban kauyawa da suka makale.

Hukumomi suka ce ruwan sama da aka yi ta tafkawa cikin kwanaki hudu ya buwayi yankin arewa maso yammacin kasar.A Afghanistan kuma, mutane 64 ne suka mutu a gabashi da arewa maso gabashin kasar, sakamakon ruwan saman.

Dakarun NATO da Afghanistan, sun ce suna amfani da jirage masu saukar ungulu wajen aikin ceto da kuma raba kayan agaji ga yankunan da bala’in ya fi shafa, da suka hada da lardunan Kunar,da kuma Nangahar.

Ahalin yanzu kuma,majalisar dinkin duniya jiya Asabar, tana kiyasin kamar ‘yan kasar Pakistan milyan daya ne bala’in ya shafa, dubban gidaje,hanyoyi da gonaki ne suka lalace.

Kakakin rundunar sojojin pakistan manjo janar Athar Abbas, ya na kashedin a sami Karin mutane da suka halaka sabo da bala’in ya taba yankuna masu yawa. Yace dubban sojoji sun ceto kamar mutane dubu 19,da yawa daga cikinsu sun dare kan jikkoki.

Ana kwashe mazauna yankin Nowshera na kasar Pakistan da mumunar ambaliyar ruwa ta yiwa barna zuwa tudun mun tsira.
Ana kwashe mazauna yankin Nowshera na kasar Pakistan da mumunar ambaliyar ruwa ta yiwa barna zuwa tudun mun tsira.

A wani lamari daban kuma,babban jami’in leken asirin Pakistan ya soke ziyarar aiki da zai kai Ingila dominn bayyana rashin jin dadin kasar kan kalaman PM Britaniya David Cameron, wan day a danganta kasar da mayakan sakai.

XS
SM
MD
LG