Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da Mutane Miliyan 7 Ke Shan Maganin Cutar HIV A Africa


Wasu kwayoyin kare cutar HIV
Wasu kwayoyin kare cutar HIV

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, yawan mutane dake karbar maganin kare cutar HIV ya karu a Africa daga kasa da miliyan daya zuwa miliyan 7.1 a cikin shekaru bakwai.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, yawan mutane dake karbar maganin kare cutar HIV ya karu a Africa daga kasa da miliyan daya zuwa miliyan 7.1 a cikin shekaru bakwai.

Bisa ga cewar Darectan kula da shirin yaki da HIV na Majalisar Dinkin Duniya, Michel Sidibé, yace “Africa ta kasa a kokarin ta na shawo kan yaduwar cutar HIV.”

A cikin shekarar da ta gabata, yawan wadanda suke shan maganin rage karfin cutar ya karu daga miliyan daya a shekara 2005 zuwa miliyan 7.1 a 2012. A shekarar da ta wuce kuma aka sami Karin mutane mliyan daya da suke shan maganin.

Rohotoni daga kasashe 16 na Afrika da suka hada da Botswana, Ghana, Gambia, Gabon, Mauritius, Mozambique, Namibia, Rwanda, São Tomé da Principe, Seychelles, Sierra Leone, South Africa, Swaziland, Tanzania, Zambia, da Zimbabwe, suna nuni da cewa, fiye da kashi uku cikin hudu na mata masu ciki dake dauke da kwayar cutar kanjamau suna samun maganin kiyaye yada cutar ga ‘ya’yansu.

Duk da wannan kokarin, mutane da yawa a kasashen Africa suna cigaba da kamuwa da kwayar cutar HIV fiye da sauran sassan kasashen duniya, banda haka kuma, nahiyar Afrika tana da kashi 69% na mutanen da ke rayuwa da cida gaba daya.

Mutane miliyan 1.8 ne suka kamu da kwayar cutar kanjamau a shekara ta 2011 a kasashen Africa, wadansu miliyan 1.2 kuma suka mutu ta dalilin kamuwa da cutar da sauran cututtuka.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG