Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Borno Sun Kira Kauracewa Ajujuwa


Gangamin dalibai a jihar Borno
Gangamin dalibai a jihar Borno

A cigaba da juyayin sace daliban makarantar 'yan mata dake Cibok a jihar Borno gamayyar daliban jihar sun kira dalibai a duk fadin duniya da su kauracewa azuzuwa gobe domin yin alhini sabili da 'yan matan da har yanzu ba'a ganosu ba.

Gamayyar daliban Borno sun kira dalibai a duk fadin duniya da su kauracewa azuzuwa gobe Laraba domin nuna alhini sabili da daliban da aka sace daga garin Cibok.

'Yan kungiyar daliban sun yi kira ne bayan taron da suka yi a Maiduguri inda suka nuna takaicinsu da sace daliban da yanzu kungiyar Boko Haram ta tabbatar cewa ita ce ta sacesu. Daliban sun ba gwamnati kwanaki arba'in gwamnati ta kubuto da yaran idan kuma ta kasa zasu kira taron kasa a Maiduguri domin nuna rashin gamsuwarsu.

Ahmed Shehu shi ne shugaban kungiyar jakadun wanzar da zaman lafiya dake wakiltan matasan dake fafitikan wanzar da zaman lafiya a arewa maso gabashin Najeriya. Yana cikin wadanda suka halarci taron. Yace su matasa da daliban su ne abun ya fi shafa domin wadanda aka sace yara ne dalibai. Yace idan basu yi wani abu ba to gobe lamarin ka iya faruwa da su. Yace dole rawar ta canza idan za'a gano daliban. Daliban suna bukatar a kauracewa azuzuwa a duk fadin duniya.

Malamai ma sun goyi bayan matakin da gamayyar daliban ta dauka musamman domin labarin da suka ji cewa a Abuja gwamnati tace a tsare shugabar makarantar Cibok wurin da aka sace 'yan matan.

Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG