Accessibility links

Gobara ta kona wani mai yin aikin walda, agarin Misau dake jihar Bauchi.

Kawo yanzu garin Misau mai zama hedkwatan karamar hukumar bata da ma’aikatan kashe gobara a karamar hukumar, idan aka samu gobara saidai a kawo dauki daga Azare.

A yau gobara ta kona wani mai yin aikin walda, agarin Misau dake jihar Bauchi, sanan ta kona wasu mutane biyar, wandanda a halin yanzu suke kwance a asibitin garin Misau.

Gobaran ya faru ne a lokacin da mai aikin waldan ke kokarin toshe tankunar wasu motocin daukar mai a harabar ma’aikatan ruwa, a garin na Misau, inji shugaban karamar hukumar ta Misau, Alhaji Muhammad Kure Misau, ya kuma kara da cewa karamar hukumar zata dauki nauyin majiyatan.

XS
SM
MD
LG