Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana ta yi bikin zagayowar ranar samun 'yancin kai gabanin ziyarar Shugaban kasar zuwa Amurka


Wata mata 'yar kasuwa a Ghana
Wata mata 'yar kasuwa a Ghana

Kasar Ghana na bukin zagayowar ranar samin ‘yancinta daga

Kasar Ghana na bukin zagayowar ranar samin ‘yancinta daga kasar Burtaniya karo na 55 da irin faretin da aka saba a Accra babban birnin kasar da kuma jawabi daga Shugaba John Atta Mills.

Babban bukin da ake yi a yau Talata a babban Dandalin ‘Yacin Kai da ke Accra za a yi irinsa a yankuna da kuma hedikwatocin gundumomin kasar.

Ministan Harkokin Gidan Ghana Fritz Baffour ya gaya wa Muryar Amurka cewa wannan wata dama ce ta sabunta damar da kasar ta samu.

Bayan shagulgulan samun ‘yancin kai, Shugaba Mills zai ziyarci Amurka, inda zai gana da Shugaba Barack Obama ranar Alhamis a Fadar White House.

Ministan Cikin Gidan ya gaya wa Muryar Amurka cewa yana kyautata zaton ziyarar za ta karfafa dangantakar Amurka da Ghana, kuma wannan ziyarar za ta amfani ‘yan Ghana.

Mr. Obama ya ziyarci Ghana a 2009 a ziyararsa ta farko zuwa Afirka kudu da Sahara a matsayinsa na Shugaban kasa. Ya ce ya tafi Ghana ne don ya karfafa tsarin dimokaradiyyarta.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG