Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Buhari Ta Bar Gwamnan Gombe


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo

Guguwar Buhari da ta wuce da gwamnonin PDP da dama a zaben 2015 ta bar Ibrahim Dankwambo gwamnan Gombe.

Yayinda guguwar Buhari ta yi awongaba da wasu 'yan siyasa musamman a arewacin Najeriya inda ta kawar da wasu gwamnonin PDP da 'yan majalisun jihohi da ma na tarayya da dama gwamnan Gombe ya rayu.

Duk da karfin guguwar bata sa al'ummar jihar Gombe kawar da gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo ba. Maimakon kawar dashi jajircewa suka yi suka sake zabarsa.

Wasu da aka zanta dasu sun bayyana dalilansu na sake zabar gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo. Malam Balarabe Shehu yace abun da ya sa guguwar Buhari bata tafi da gwamnan ba iko ne na Ubangiji. Amma gwamnan ya yi aiki. Ya gyara harkar ilimi. Ya gyara makarantu 128 ya kuma kirkiro wasu sabbi. Ya baiwa ilimi gagarumin gudummawa yadda nan gaba za'a ci moriyar abun da ya yi.

Usman Shehu cewa ya yi Alhaji Ibrahim Dankwambo ya zauna lafiya da jama'a. Ya mutunta jama'a. Ya kuma yiwa jama'a ayyuka. Ya kuma kyautatawa kowa saboda haka idan ya ci zabe ba abun mamaki ba ne.Yace a lura, tunananen mutane ya canza haka ma alkiblarsu. Yanayin siyasa a Najeriya ya canza. Dabarun da na zage-zage da muzgunawa mutane basu da tasiri kuma. Yace siyasa yanzu ita ce yaya ka rike al'ummarka.

Hajiya Fati Kulani tace dole ne su fito su sake zabar Ibrahim Dankwambo saboda yadda ya yi da 'ya'yansu. Ya samar masu aiki. Ya sa 'ya'ya sun shiga taitaiyinsu inda suka daina sare-sare. Ya sasu sun san darajar iyaye. Dalili ke nan da ya sa mata suka fito kwansu da kwarkwatarsu su yiwa Dankwambo sakayya.

Abdulkadir yace su yau sun godewa Allah "domin komin duhun dare hannu ba zai manta da baki ba"-inji shi. Allah ya tabbatar cewa shi yake bada mulki ba wadanda suke ganin su ne suka nadawa ba. Suna godiya Allah ya sake zabar Ibrahim Hassan Dankwambo.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG