Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Babangida Aliyu kan Taron Gwamnonin Arewa


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Gwamnonin jihohin arewa sun yi wani taro jiya a Abuja babban birnin Najeriya.

Da yake magana da wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu yace abubuwa biyu suka tattauna a taron nasu. Abu na farko shi ne kan taron da gwamnonin arewa suka je yi a nan Amurka. Yace sun tattauna da gwamnatin Amurka irin taimakon da za'a ba arewa domin shawo kan tashin tashinar da arewa ke fama dasu. Sun yi batun kashe-kashe da suka addabi arewa da kuma tabarbarewa tattalin arziki. Su Amurka suna son su san hanyoyin da zasu kara taimakawa arewa. Yace dama can suna yi amma yanzu suna son su gano hanyoyin da zasu yi anfani da su a kawar da abubuwan dake damun arewa.

Akwai wasu taimako da ba za'a iya fada a fili ba inji shi gwamnan. Amma akwai taimako kan harkokin ilimi da sha'anin noma da sha'anin kiwon lafiya da dai sauransu zasu kara.

Sai kuma batun taron kasa da ake yi yanzu. Gwamnan yace dama akwai abubuwan dake damun arewa suna kuma son su tabbatar an gabatar dasu. Yace taron nasu yana son ya jawo hankalin wadanda ke wakiltar arewa su san matsalolin dake addabar yankin kada a gama taron basu fito dasu ba. Yace daga lokaci zuwa lokaci zasu dinga yin taro dasu domin su tabbatar sun gabatar da manufofin arewa da abubuwan da suka damu arewa.

Arewa nada bukatu da yawa. Na daya yadda ake raba arzikin kasar nan arewa bata gamsu ba. Abu na biyu shi ne harkar tsaro. Yace tun lokacin da sojoji suka karbi mulki sai harkokin tsaro suka koma hannun gwamnatin tarayya.Yace a jiharsa yana da kwamishanan 'yansanda amma a matsayinsa na gwamna duk abun da kwamishanan zai yi sai ya hada da Abuja inda za'a bashi oda. Ana cewa gwamna shi ne shugaban tsaro a jiha amma babu abun da zai iya yi sai abun da manyan Abuja suka ce. Kwamishanan 'yansanda baya jin wani gwamna sai shugabannin dake Abuja. Gwamnonin arewa suna neman taron kasa ya warware wannan lamarin. Taron kasa kuma ya gyara yadda ake raba arzikin kasar. Yakamata a rage kason da gwamnatin tarayya ke samu domin jama'a a jihohi suke. Sha'ani ilimi , asibiti, noma da dai sauransu a mayarda su inda jama'a suke, wato jihohi.

Ga firar Medina Dauda da Gwamna Aliyu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG