Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Imo Ya Ziyarci Majalisar Dokokin Kano Akan Yaki da Ta'adanci


Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha
Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha

Gwamnan jihar Imo Rochas Okororcha ya kai ziyara Majalisar Dokokin Jihar Kano saboda neman hadin kan duk 'yan APC su tashi su taimaka wurin yaki da kungiyar Boko Haram da ta'adanci a kasar.

Yayin ziyara da ya kai majalisar dokokin Kano gwamnan ya tattauna da 'yan majalisar akan mahimmancin 'yan jam'iyyarsu ta APC su samu hadin kai domin kawar da kungiyar Boko Haram da duk wani aikin ta'adanci.

Yaki da 'yan Boko Haram ko ta'adanci ba na shugaban kasa ba ne kawai. Kamata ya yi su hada kai domin a samu a kawar da matsalar.

Furucin na gwamna Imo ya sa masana harkokin tsaro da shari'a suka yi tsokaci akan kwamitin nan na gwamnonin arewa da suka dorawa alhakin zakulo masu tallafawa 'yan kungiyar ta Boko Haram da wasu dake aiwatar da ta'adanci musamman a arewa maso gabashin Najeriya.

Keften Abdullahi Adamu Bakoji mai ritaya yace a ganinsa harkar tsaro shi ne a sallamawa jami'an tsaro shi zai kawo mafita. Babu yadda gwamnoni zasu iya zakulo masu tallafawa 'yan ta'ada sai sun hada da jami'an tsaro. Jami'an tsaro sun san yawancin abubuwa. Sun san 'yan siyasa. Sun san 'yan ta'ada. Idan an basu dama zasu zakulosu ba sai gwamnoni sun wahalar da kansu ko bata dukiyar jama'a ba.

Shi kuwa Barister Audu Bulama Bukarti cewa ya yi idan an yi la'akari da dokokin Najeriya ta'adanci al'amari ne da ya shafi kasa baki daya. To duk abun da za'a yi ya zama karkashin shugaban kasa da kuma gwamnatin tarayya. Batun zakulo wadanda suke tallafawa ta'adanci dokar 2013 ta yi bayani dalla dalla inji Barrister Bukarti. Ita ma hukumar EFCC akwai ikon da dokar ta bata dangane da kudaden ta'adanci. Barrister Bukarti yace saboda haka idin gwamnoni nada wata shawara da zata taimaka kamata ya yi su rubutawa shugaban kasa wasika su yi bayani.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG