Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Borno Ya Gabatar da Amina Ali wa Shugaba Muhammad Buhari


Amina Ali da jaririyarta da gwamnan Borno
Amina Ali da jaririyarta da gwamnan Borno

Jiya tawagar gwamnan Borno ta isa Abuja inda gwamnan ya gabatar da Amina Ali 'yar makarantar Chibok da Allah ya ceceta ta hannun sojojin Najeriya daga kungiyar Boko Haram da ta sacesu .

Tawagar gwamnan Borno ta isa Abuja jiya inda gwamnan ya gabatarda Amina Ali wa shugaban kasa Muhammad Buhari.

Ita dai Amina Ali tana cikin daliban makarantar 'yan mata da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace daren goma sha hudu ga watan Afirilun shekarar 2014 yayinda suke shirin rubuta jarabawar sauke karatun sakandare a garin Chibok.

Gwamnan ya shaidawa shugaban kasa cewa jajircewar yarinyar, dauriya da jimrewa suka sa ta rayu har ta kai lokacin da Allah ya sa aka kubutar da ita.

'Yan Boko Haram sun yiwa Amina auren dole har ma ta haifi yarinya jaririya wadda take rike da ita a hannun.

Da murna tare da yiwa Allah godiya da sojojin kasar Shugaba Buhari ya marabci Amina, diyarta, mahaifiyarta, gwamnan Borno da sauran jami'an tsaro da na gwamnati. Shugaba Buhari ya jadda cewa gwamnatinsa ba zata amince da auren dole ba.

Ga karin bayani

Gwamnan Borno Ya Gabatar da Amina Ali wa Shugaba Mumhammad Buhari
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG