Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamanan Jihar Borno ya Ziyarci 'Yan Gudun Hijira Dake Garuruwan Adamawa


Gwamna Kashim Shettima
Gwamna Kashim Shettima

Bayan hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a wasu garuruwan jihar Borno dubun dubatan mutane suke fice daga gidajensu zuwa neman mafaka a garuruwan Adamawa lamarin da ya sa gwamnan jihar Bornon ya ziyarcesu.

Gwamnan Jihar Borno ya je jihar Adamawa domin gani da idanunsa irin halin da mutanen da 'yan Boko Haram suka kaiwa hari musamman a garin Izge jihar Bornon.

'Yan gudun hijiran dake tsugune a garuruwan Gulak da Madagali jihar Adamawa sun hada da mata da yara wadanda suka zama abun tausayi. Wakilin Muryar Amurka da shi ma ya kai ziyara ya ga yara suna kuka mata kuma suna kwalla dukansu cikin halin lahaula wala kawati.

Yayin da gwamnan ya je garin Gulak shi ma yana magana yana kwalla ganin irin halin da mutanensa suka fada ciki musamman idan an yi la'akari da cewa wadannan mutane ne da basu ci ba basu sha ba.

A jawabin da gwamna Kashim Shettima ya yi masu ya basu hakuri. Ya fada masu cewa su ma sun damu da abun da yake faruwa a jihar. Ya ce da can gwamnati ta bada taimakon nera miliyan dari daya. Yanzu kuma ta kara nera miliyan dari daya. Sanata Ndume yana cikin tawagar da ta ziyarci 'yan gudun hijiran. Yace kowa ya san abun da ya kawo su domin haka suna ba mutane hakuri da bada tabbacin taimako daga kwamnati.

Gwamnan ya ziyarci sarkin garin wanda yace kawo yanzu duk mutane kauyukan sun gudu domin banda kashe-kashe gidajensu ma an konesu tare da gonakansu. Wuraren ibada ma basu tsira ba domin maharan sun kone masallatai da coci coci.

Ga Haruna Dauda Biu da cikakken rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG