Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Bada Gaske ta Keyi Ba Akan Yakar Boko Haram


Waasu 'yan gudun hijira a Borno
Waasu 'yan gudun hijira a Borno

A wata fira da yayi da Muryar Amurka Sanata Ali Ndume mai wakiltar kudancin jihar Borno yace gwamnatin Shugaba Jonathan ba da gaske ta keyi ba akan yakar kungiyar Boko Haram.

Sanata Muhammed Ali Ndume yace gashi siyasa ta soma yin zafi a wasu wurare amma kuma ga halin da wasu jihohi uku na arewa maso gabas suke ciki.

Abun da shi ya fi mayar da hankalinsa akai shi ne yadda gwamnati zata dawo masu da zaman lafiya a yankunansu. Idan babu zaman lafiya duk abun da za'a yi ya zama banza.

Akan ko za'a iya gudanar da zabe a jiha irin Borno kamar yadda za'a yi a kudancin kasar, Sanata Ndume yace ba ya tsammanin za'a iya yin hakan amma kowane irin hali ake ciki yakamata a gudanar da zaben.

Idan har gwamnati ba zata iya kawo zaman lafiya a yankunasu ba to su da suke gudun hijira a wasu wurare cikin jihar Borno yakamata a tanada masu su yi zabe a wuraren da suka samu kansu.

Dangane da 'yan kananan hukumomi kamar bakwai ko takwas da basa matsuguninsu suna nan baze a sansanoni daban daban ta yaya hukumar zabe zata iya gudanar masu da zabe. Sanata yace zai koma majalisa domin a sake dokar zabe ta yadda zata ba mutane dake gudun hijira dama su yi zabe inda suke.

Idan bata mayarda mutane gidajensu ba sabili da rashin tsaro to kamaya yayi ta basu izinin yin zabe inda suke. To saidai Sanata Ndume yace gwamnatin tarayya bata da niyyar tunkarar 'yan Boko Haram domin a samu zaman lafiya. Gwamnati bata yin abun tsakaninta da Allah.

Idan gwamnati tana yin yaki da Boko Haram tsakaninta da Allah tana da karfin da zata iya kawo karshen ta'adancin Boko Haram. Najeriya nada sojoji fiye da dubu dari amma 'yan Boko Haram basu kai dubu goma ba. Idan da gaske ake yi kowadane sojojin Najeriya goma zasu yaki dan Boko Haram guda daya kacal.

Sanatan ya kira gwamnati ta tashi tsaye tayi yakin tsakaninta da Allah. Shugabanni su dauki alhakin da ya rataya akansu tsakaninsu da Allah. Su yi abun da yakamata domin kawo karshen tashin hankalin cikin dan karamin lokaci. Idan ba'a yi tsakani da Allah ba to ana da muguwar niyya ke nan.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG