Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Bata Samu Dattawan Zahiri da Zata Tattauna da Su Ba Akan Rikicin Niger Delta


Shugaba Mohammadu Buhari
Shugaba Mohammadu Buhari

Tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriya da dattawan yankin Niger Delta ta gagara domin shugaban Najeriya Muhammad Buhari yace ba'a samu dattawa na zahiri ba da zasu tattauna da gwamnati.

To saidai a wani bangaren wadanda suke kiran kansu dattawan yankin na Niger Delta na cewa hakurinsu ya kusa karewa da gwamnatin Najeriya.

Su kuma 'yan bindigan yankin sun yi ikirarin shirya damarar komawa kai hare-hare kamar na da can kan kamfanonin dake hako man fetur a yankinsu.

Amma bayanai daga fadar shugaban kasa ta bakin mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu yace tattaunawa da dattawan yankin na Niger Delta tana nan.

Yace ba wai an fasa maganar ba ne. Tana nan ana yi amma su dattawan yankin so suke son sai sun zo sun zauna da Shugaba Buhari ida da ido kafin su san da gaske gwamnati ta keyi. Yace akwai manyan jami'an gwamnati irinsu karamin ministan man fetur da shugabannin kamfanoni da na gwamnati a tattaunawar.

Inji Garba Shehu gwamnatin Buhari tana iyakacin kokarinta kuma da yaddar Allah ba za'a ji kunya ba.

Janar Rabe Abubakar mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya ya bayyana irin matakan da suke dauka. Yace hakkinsu ne su kare dukiyoyin Najeriya ko ta halin yaya.

Kwamando Baba Gamawa yace tattaunawa da dattawan yankin ya zama tamkar wasan yara saboda bayan an tattauna da wasu tattawan sai wasu kuma su fito su ce basu yadda ba. Haka ma wata daga yankin tace dattawansu basa magana akan matasan, a'a akan nasu muradun suke tattaunawa.

Ga rahoton Lamido Abubakar da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG