Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Israila Na Shirin Takaita Shige da Ficen Falasdinawan Gabashin Qudus


Falasdinawa suna komawa gabshin birnin Qudus bayan sallar Juma'a ta ranar Oktoba 23, 2015
Falasdinawa suna komawa gabshin birnin Qudus bayan sallar Juma'a ta ranar Oktoba 23, 2015

Gwamnatin Israila Na Shirin Takaita Shige da Ficen Falasdinawa dake Gabashin Qudus tare da hanasu wasu abubuwan more rayuwa da yin walwala

Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu yana tunanen takaita wasu anfani da Falasdinawa suke cn moriyarsu daga Israila.

Kazalika Mr. Netanyahu zai takaita zirga zirgan da Falasdinawa dake zama a gabashin birnin Qudus su keyi, wato zai rage tafiye tafiyensu. Matakan tamkar mayarda martani ne akan yadda Falasdinawan suke cigaba da tada rikici tsakaninsu da jami'an tsaron Yahudawa..

Jami'an Israila sun fada jiya Litinin cewa tuni Mr. Netanyahu ya bada umurnin a yi nazari akan abubuwan jin dadi da na zamantakewa da Falasdinawa ke samu a gabashin birnin Qudus. Abubuwan da Falasdinawan dake gabashin Qudus ke samu Falasdinawan dake West Bank basa samunsu. Abubuwan ne Netanyahu yake shirin hanasu ko ragesu tare da takaita shige ta ficensu a birnin Qudus.

Rikici tsakanin Yahudawa da Falasdinawa ya barke ne watan jiya a masallacin al-Aqsa. Yahudawa 10 suka rasa rayukansu tunda rikicin ya fara ta hanyar sukansu da wuka. A bangaren Flasdinawa kuma su 51 jami'an tsaron Israila suka harbe har lahira tare da raunata wasu 30 da Yahudawa suka ce masu kai masu hare-hare ne.

XS
SM
MD
LG