Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin JIhar Borno Zata Kwaso 'yan gudun hijirar Dake Kan Iyaka


'Yan gudun hijira kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
'Yan gudun hijira kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Gwammnatin jihar Borno ta fara kwashe ‘yan gudun hijira daga jihar da kasar Kamaru ta tasa kyeyarsu . sama da ‘yan gudun hijira dubu biyu ne aka tasa keyarsu zuwa Najeriya bayan sun ketara kasar Kamaru domin gujewa hare haren kungiyar Boko Haram.

Akasarin ‘yan gudun hijiran da aka koro daga kasar Kamaru ‘yan asalin jihar Borno ne wadanda suka kauracewa matsugunansu sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram da ya tilasta su fantsama kasashen Kamaru da Chadi dake makwabta da jihar Borno ,kafin daga bisani kasashen biyu suka tasa keyarsu suka jibge su kan iyaka ba tare da an yi wani shirin sake tsugunar da su ba. Lamarin da hukumomin bada agaji a Najeriya suka ce bai dace ba,

A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdul’aziz, ‘yan gudun hijiran sun bayyana gamsuwa da matakin da gwamnatin jihar Borno ta dauka na sake masu matsuguni.

A nashi bayanin, Alhaji Aliyu Yarima jami’in tuntuba na jihar Borno, yace, ana kyakkyawan kulawa da ‘yan gudun hijira wadanda yace suna cikin koshin lafiya kuma ana basu abinci isasshe a kalla sau uku a wuni.

Hukumomi da al’umma na ci gaba da bayyana rashin gamsuwa dangane da tasa keyar ‘yan gudun hijirar da gwamnatin kasar Kamaru tayi musamman ganin ziyarar da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya kai kasar Kamaru da nufin neman hadin kan kasar a yaki da kungiyar Boko Haram ,da kuma tsugunar da ‘yan gudun hijira.

Ga cikakken rahoton

'Yan Gudun HIjiran Najeriya-2:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG