Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Filato Ta Gaji Dinbin Bashi


Gwamnan jihar Pilato Simon Lalon yace ya yanzu sun bankado cewa gwamnatin data shude na Jonah Jang ta bar musu bashin naira biliyan104. A tattaunawar da gwamnan yayi da rediyon Muryar Amurka ya yace gwamnatin sa ta nada kwamiti da zai bi diddigin basussukan da gwamna Jonah Jang ta bari da kuma matakan da sabuwar gwamnati zata dauka.

‘’Ta bar mana bashin kusan biliyan 104 ba a gama bama ana zaton idan aka gama zai karu kuma abinda ya bani mamaki shine abinda za a bar gwamnatin da zata shiga wato namu gwamnatin shine miliyan 90, miliyan 90 bai ma isa ya biya maaikata guda daya ba a jihar Pilato, kuma muna bukatar bilayan ne da yawa wanda zamu biya maaikata to abinda na gani ya kawo muna damuwa ke nan dole ne a duba domin kudi na jamaa ne ba za a bar kudi su tafi haka ba, yanzu munsa a bido muna ainihin basussukan da aka bari da kuma ainihin kudaden da yakamata a bari, dole mun fuskanci abinda zamu yi ayi gyara sabo da gobe.Ba wai ana neman ayi fada bane ko ace ana fada da wanda ya bar gwamnati bane a’a, dominkayan gwamnati kayan jamaa ne dole ne mu lura dashi, mu duba inda kudade suka fita inda kudade suka bata domin a dawo dasu domin mu samu gyara, ba zamu waiwayi baya ba’’

Akwai wadansu matakai da zaka dauka wajen ganin ka kara hada kan jamaa kila ko ta wajen tattaunawa da wadanda basu gamsu da gwamnatin data wuce ba?

‘’Kwarai domin bamu gama nade-nade ba, a lokacin da muka gama zasu lura cewa duk abbuwan da muke yin a hadin kai ne kuma banda haka mun riga munsa a kasa munce ko wane kabila zata samu shiga a wannan gwamnati idan ba wani abu ba da ikon ALLAH zamu bi duk hanyoyi da kowa zaiji dadi ya samu jin dadin zaman lafiya a pilato’’.

Sai wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji ta kasa samun wanda zai mayar da martini daga bangaren tsohon gwamnan.

Gwamnatin Jihar Filato Ta Gaji Dinbin Bashi - 2'44"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

XS
SM
MD
LG