Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kasar Kwango Zata Tattaunawa Da 'yan Tawayen M23


Mayakan 'yan tawayen M23
Mayakan 'yan tawayen M23
Gwamnatin Kwango-Kinshasa ta bayarda sanarwar shirye-shiryen fara tattaunawa da kungiyar ‘yan tawaye ta M23, wadda ta kwace garin Goma na gabashin kasar a watan da ya shige, kafin ta yarda ta janye a makon da ya shige.

Ministan harkokin cijkin gidan Kwango, Richard Muyej, yace za a fara wannan tattaunawa cikin ‘yan kwanaki kadan a Kampala, babban birnin Uganda.

A ranar litinin, sojojin gwamnatin Kwango sun koma garin Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa, a bayan janyewar ‘yan tawaye a karshen makon da ya shige. Amma kuma, kungiyar M23 ta yi barazanar zata sake komowa ta kwace garin na Goma idan har gwamnati ta ki cika alkawarin da ta yi na tattaunawa.

Kungiyar M23 ta kunshi tsoffin ‘yan tawayen da aka shigar cikin rundunar sojojin kasar Kwango. ‘yan tawaye sun janye daga cikin rundunar sojojin kasar a wannan shekarar, su na kukar cewa ana musgunawa tare da nuna musu rashin kauna.

Tun lokacin da kungiyar ta fara tawaye a watan Afrilu, ta ba sojojin gwamnati kashi a lokuta da dama, ta kuma kwace yankuna da dama na lardin Kivu ta Arewa.
XS
SM
MD
LG