Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kasar Nijer Ta Mika Sakon Ta'aziya Ga Al'ummar Kasar Afirka Ta Kudu


Mr. Morou Amadou kakakin gwamnatin kasar Nijer kuma ministan shari'a
Mr. Morou Amadou kakakin gwamnatin kasar Nijer kuma ministan shari'a

Kakakin gwamnatin kasar ta Nijer kuma ministan shari'a Morou Amadou ne ya isar da sakon hukumomin kasar a wani taron manema labarai da ya yi jumma'a a birnin Niamey

Gwamnatin kasar jamahuriyar Nijer ta nuna juyayin ta tare da yin ta'aziya ga al'ummar kasar Afirka Ta Kudu dangane da rashin tsohon shugaban kasar Nelson Mandela gwarzon yaki da wariyar launin fata, kuma bakar fatar farkon da yayi shugbancin kasar.
A wata ganawa da yayi da manema labarai kakakin gwamnatin kasar Ministan shari'a Morou Amadou ya bayyana Mandela da cewa shugaba ne da ya bar tarihin da ya zama abun koyi ga shugabannin kasashen Afirka. Wakilin Sashen Hausa Abdoulaye Mamane Amadou ya halarci taron na manema labarai, kuma ya aiko jawabin yabo da karrama marigayi Nelson Mandela da kakakin gwamnatin kasar ta Jamahuriyar Nijer Morou Amadou yayi kamar haka:

Kakakin gwamnatin jamahuriyar Nijer Morou Amadou - 2:09
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG