Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Nada Karfin Gwiwar Kubutarda Yaran Chibok


‘Yan Sanda na lura da yadda zanga-zangar Chibok ke gudana a gaban ofishin Jakadancin Najeriya a Washington D.C. (File Photo)
‘Yan Sanda na lura da yadda zanga-zangar Chibok ke gudana a gaban ofishin Jakadancin Najeriya a Washington D.C. (File Photo)

Yayin da al'ummar Najeriya suka sa ido su ga yadda gwamnatin kasar zata kubutarda yaran Chibok, gwamnatin ta fito tace tana samun nasara ta samun bayanai akan kokarin da ake yi na kubuto da yaran.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bakin ministan yada labarai Labaran Maku ta tabbatar cewa tana samun nasarori na bayanai gameda ayyukan da jami'an tsaronta su keyi domin kubutarda 'yan matan nan da kungiyar Boko Haram ta sace suka kuma yi garkuwa dasu fiye da wata daya da ya gabata.

Wannan bayanin da ministan yada labarai yayi ya zo daidai da lokacin da bincike ya nuna cewa shugaban kasa Goodluck Jonathan yana ta yin taruruka tun shekaranjiya da dare da jami'an tsaron kasar domin kara samun bayanai da kuma daukan matakan da suka kamata domin kubutar da yaran daga mugun hannun da suke ciki yanzu.

Bayan da aka kammala taro na mako-mako na majalisar ministocin Najeriya, Labaran Maku yayi karin haske akan irin habbasan dake gabansu da kuma irin kalubalen da jami'an tsaron kasar ke fuskanta a kokarin kubutar da yaran.

Ministan Mr. Labaran Maku yace har yanzu suna kan nazarin hanyoyin da zasu bi da fatan Allah Ya basu nasara su dawo da yaran gidajensu lami lafiya. To saidai yace abu ne mai wuya. Yadda za'a fitar da yaran da ransu shi ne babban aiki domin wadanda suke rike da yaran zuciyarsu ta riga ta mutu. Suna iya su yi abun da bai kamata ba. Amma duk jami'an tsaro suna nan akan aikinsu. Suna kuma bada rahoto akan kokarinsu. Ministan ya kira al'ummar Najeriya ta hada kai da jami'an tsaro musamman mutanen dake jihohin arewa maso gabas.

To saidai bayanai na fitowa daga kafofin yada labaru cewa ana zargin wasu manyan sojojin kasar da hannu a wurin bada makai da horo da bada bayanai ga kungiyar Boko Haram lamarin da ya kai har aka gurfanar da janarori sama da goma sha biyar a gaban kotun sojoji inda ake yi masu shari'a.

Akan rahoton kakakin rundunar sojojin na kasa Birigediya Janar Olu Kolade yace labaran dake fitowa daga kafofin labarai ba gaskiya ba ne. Shi ma Labaran Maku yace bashi da tabbatacen bayani ko masaniya akan batun. Duk da musantawar bayanai dake fitowa daga wasu kafofin gwamnati suna gasganta labarin.

Irin wadannan bayanan da suka sa 'yan kungiyar Boko Haram na samun bayanan siri yasa askarawan kasashen waje basu cika yin isgilancin shigowa kai tsaye cikin Najeriya su yi aikin ba.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:02 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG