Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ce Har Yanzu Saudiyya Bata Biya Diyyar 'Yan Najeriya 6 Ba


Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu gwamnatin Saudiyya bata biya diyyar mutane shidda ‘yan Najeriya da kugiyar daukar kaya ta fado masu lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar su a masallacin Ka’aba a shekarar data gabata.

A wani taron masu ruwa da tsaki akan hawan arfa na wannan shekarar, mai rike da mukamin jakadan Najeriya a kasar ta Saudi’arabiya ambasada Salisu Ummar, ya ce kawo yanzu babu wani bayani daga kasar ta Saudiyya amma suna ci gaba da tuntubar gwamnatin kasar.

Taron ya sami halartar dukkan masu ruwa da tsaki akan aikin hajji daga bangaren Najeriya. A cikin jawabin da ya gabatar Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar, ya jaddada matsayinsa na Amirul Hajjin Najeriya na wannan shekara, al’amarin dake zaman mayar da martani ga Alhazan Najeryar data kira shi shugaban majalisar koli ta addinin musulunci a wajan aikin Hajjin.

A jawabinsa ya bayyana cewa tawagar bat azo ne domin sanya ido ko kuma bincike akan ayyukan hukumar alhazan ba, amma ta zo ne domin bada shawara a matsayinsu na shugabannin musulunci na Najeriya.

Dr Aliyu Tanko dake zaman daya daga cikin jami’an hukumar Alhazan Najeriyar ya yi bayanin cewa bashi da tacewa gaya ga bayanin da shugaban tawagar yayi, kamar yadda yace idan Allah ya yarda bayan sun koma gida za’a gyara dukkan matsalolin.

A baya dai gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta soke bayar da tallafi ga maniyyata aikin Hajji tare da daukar dawainiyar Amirul Hajjin.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari Daga Saudiyya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG