Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Zata Kara Tsaurara Matakan Tsaro A Sansanonin 'Yan Gudun Hijira


Sansanin 'yan gudun hijira a Bama.
Sansanin 'yan gudun hijira a Bama.

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace zata kara tsaurara matakan tsaro a sansanin ‘yan gudu hijira. Bayan da wasu ‘yan kunar bakin wake su biyu suka tada bomb a sansanin dake Dikwa, wanda yayi musabbabin mutuwar ’yangudun hijra har su 58.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, shine yayi wannan alkawarin a jiya Laraba, yana cewa wai ‘yan ta'adda su rasa inda zasu kai hari sai inda bayin Allah da irin wannan mummunar dabi'ar ta ‘yan ta'adda ya raba da matsugunnin su maimakon su zame abin tausayi na irin halin da suka shiga amma kuma an koma sune ake kara gallazawa.

Yace tilas gwamnati ta samar da tsaro mai tsananin gaske a duk inda sansanin ‘yan gudun hijira yake.

Jami'an gwamnatin kasar suka ce wasu mata masu tayar da kayar baya ne su uku suka yi shigan burtu, a matsayin ‘yan gudun hijira suka shiga cikin sansanin biyu daga cikin su suka tarwatsa kansu, ita kuma ta ukun ta sake shawara bayan ta fahinci cewa iyayen da ‘yan uwan ta na cikin sansanin, sai ta mika kanta ga ‘yan sanda.

Sai dai ba wanda ya dauki alhakin wannan ta'asar amma dai anfi danganta shi da kungiyar Boko Haram.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG