Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Neja Ta Cafke Wasu Jami'an Tsohuwar Gwamnatin Jihar Bisa Zargin Sata


Dr. Babangida Aliyu tsohon gwamnan jihar Neja wanda a karkashinsa ne jami'an suka yi aiki
Dr. Babangida Aliyu tsohon gwamnan jihar Neja wanda a karkashinsa ne jami'an suka yi aiki

Sabuwar gwamnatin jihar Neja ta kama wasu manyan jami'an tsohuwar gwamnatin Babangida Aliyu saboda wai sun yi sama da fadi da kudi nera miliyan dari biyu da miliyan dari tara ko biliyan biyu da digo tara

Jami'an guda biyar ana zarginsu da wawure kudin gwamnati N2.9b a lokacin da suke mulki a karkashin gwamna Babangida Aliyu.

Tsoffin jami'an da aka cafke sun hada da manyan sakatarori guda uku da tsohon shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin jihar da kuma wani tsohon shugaban karamar hukuma.

Kwamishanan 'yansandan jihar Alhaji Abubakar Marafa yace wani kwamitin siri ne da gwamnatin jihar ta kafa domin bankado kudaden da aka kashe ba akan kaida ba ya tono badakalar. Kwamitin ya kunshi 'yansanda da SSS da jami'an gwamnatin jihar.

Kawo yanzu kakakin gwamnan jihar Jibril Baba Ndache yace ko bayan guda biyar din da aka cafke akwai wasu da dama da suke bincike. Ndache yace ana cigaba da bincike kuma ana kiransu a yi masu tambayoyi kuma duk inda aka tabbatar an yi ba daidai ba dole a kwato kudaden a yiwa jama'a aiki dasu.

Wadanda suka amsa laifin sun soma dawo da kudaden da suka handame. To amma har yanzu tsohon gwamnan jihar Babangida Aliyu bai ce komi ba akan batun. To saidai Alhaji Muhammad Sani na hannun daman tsohon gwamnan yace lamarin bita da kuli ne kawai irin na siyasa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG