Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Ce Masu Hakar Zinare Su Fice Daga Yankin Jado


Wani wajen hakar zinare
Wani wajen hakar zinare

Gwamnatin Nijar ta baiwa masu hakar zinari wa'adin daga na zuwa daya ga watan Maris da su fice daga yankin Jado da suke hakara ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Masu hakar zinari a yankin Jado dake jihar Agadaz, a Jamhuriyar Nijar, sun fara barin wajen, biyo bayan wa'adin da gwamnatin ta ba su.

Sai dai mahakan sun koka da rashin aikin yi idan har aka kore su daga wannan wuri, suna masu cewa ba su da wata hanyar ciyar da iyalansu, lura da cewa ba lokacin damuna ba ne.

Tuni dai wata tawaga da ta hada da Ministan ma’adainai Musa Baraje da shugaban hukumar wanzar da kwanciyar hankali Kanal, Abu Tarka, ta isa Jado, inda ta yi wa jama’a bayani kan yadda ‘yan kasashen waje suka fi amfana saboda sun mallaki kayan aiki, laamrin da mahakan suka amince da shi.

Saurari rahoton wakiliyar Muryar Amurka, Tamar Abari domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG